Yan ta´ada sun kashe wani dan majalisa a Labanon | Labarai | DW | 12.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan ta´ada sun kashe wani dan majalisa a Labanon

Kasashe da kungiyoyi daban daban na dunia na ci gaba da Allah wadai, da harin ta´adanci da da ya hadasa mutuwar wani dan majalisa kuma dan jarida ,a sahiyar yau a birnin Beyruth na kasar Labanon.

Gebrane Tueni, ya rasa ran sa a yayin da motar sa ta tarwatse sakamakon bom da aka nada mata.

Bom din yayi sanadiyar karinmutuwar wasu mutane 3,

Kazalika mutane 6, sun ji mumumar raunuka.

Wannan hari ya wakana, a jajibirin taron komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia, a game da sakamakon binciken da a ka gudanar, a kan mutuwar Raffik Hariri, tsofan Praministan Labanon ,wanda shima a ka kashe, a harin ta´adanci makamancin wannan, a watan Februaru da ya wuce.

Daga wannan lokaci ya zuwa yanzu , wannan shine hari na 13, da yan takiffe su kai wa kasar Labanon, wanda kuma a ke zargin Sirya, da kitsawa.

Jim kadan bayan abkuwar harin hukumomin Syria su ka yi Allah wadai da shi, domin a cewar su zai kara tsaiko, ga yunkurin da ake na tabatar da zamman lahia a kasar Labanon.

Hukumomi Labanon sun kira ga majalisar Dinkin Dunia ta buda bincike, domin gano mutanen da ke da hannu a ciki.

Kasashen Amurika , da kungiyar Gamayya Turai, Majalisar Dinkin Dunia, da Hukumar Francophonie, baki daya sun yi Allah wadai da saban harin.