’Yan ta kifen Ƙungiyar Hamas, sun yi barazanar kai hare-hare cikin Isra’ila.
July 2, 2006A wata sabuwa kuma, rukunin ’yan ta kife na kungiyar Hamas, ya mai da martani ga Isra’ilan da yin barazanar kai wa ƙasar bani Yahudun sabbin hare-hare a cikin harabobinta. Ƙungiyar ta kuma yi Alllah wadai da nuna ƙarfin sojin da Isra’ilan ke yi wa Falasɗinawa a zirin Gaza.
A halin yanzu dai, ƙungiyoyi uku da ke ikirarin yin garkuwa da sojan Isra’ilan, sun ce suna bukatar a sako fursunonin Falasɗinawa dubu ne da Isra’ilan ta ɗaure a gidajen yarinta. Amma Firamiya Ehud Olmert ya lashi takobin cewa, gwamnatinsa ba za ta miƙa wuya ga ’yan ta’adda ba. Rikicin baya-bayan nan tsakanin Isar’ilan da Falasɗinawa ya ɓarke ne, bayan da mayaƙan ƙungiyoyin Falasɗinawan suka kame wani cofur na sojin Isra’ilan, Gilad Shalit, mai shekaru 19 da haihuwa, a ran 25 ga watan jiya, a wani harin da suka kai wa rukuninsa a kan iyakar zirin Gaza da ƙasar bani Yahudun.