Yan ta kife a Najeriya sun sake kai hari kan bututun mai | Labarai | DW | 20.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan ta kife a Najeriya sun sake kai hari kan bututun mai

Kungiyar yan ta kife a Najeriya da ta sace turawa 9 kuma a yankin Naija delta,tace ta sake kai hari akan wuraren hako mai a yankin,wadda tace ya haddasa rage kashi 20 cikin dari na mai da ake hakowa a kullum.

Kungiyar da ta kira kanta mai fafutukar yantar da yankin Naija Delta,ta aika ta internet cewa,ta kai hari kan jiragen ruwan kanfanin mai na Shell amma tace babu wanda ya samu rauni.

A karshen mako ne dai yan kungiyar suka kai hari akan bututun mai da iskar gas mallaka kanfanin Shell,wanda ya tilastawa kanfanin rage kusan ganga 500,000 cikin mai da take hakowa a kullum.