Yan siyasar kasar Iraqi sun bukaci janyewar sojin taron dangi | Labarai | DW | 22.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan siyasar kasar Iraqi sun bukaci janyewar sojin taron dangi

Taron kungiyar kasashen larabawa wanda aka gudanar a birnin alkahira domin sasanta alúmar Iraqi ya bukaci janyewar sojin Amurka dana Britaniya daga kasar ba tare da wani jinkiri ba. Taron wanda ya sami halartar manyan yan siyasar kasar Iraqin dana yan adawa tare da manyan maluma, sun yi kokarin warware sabanin dake tsakanin su inda kuma suka cimma matsaya ta baiyana bukatar tsayar da takamammiyar rana da sojin Amurka dana Britaniya zasu fice daga kasar. Sakataren kungiyar kasashen larabawa Amr Moussa yace wannan dan ba ne a kokarin samun masalaha a kasar Iraqin. Bugu da kari taron ya yi Allah wadai da hare haren da ake kaiwa akan fararen hula da hukumomin gwamnati, kana ya yi kira da babbar murya da a sako dukkan mutane da ake tsare da su ba tare da jinkiri ba. Shugaban majalisar malamai na kasar Iraqin Harith al – Dhari ya kakkausar suka jamián tsaron kasar Iraqi wadanda ya ce suna koyi da akidar Amurka ta azabtar da jamaá da kame su ba tare da wani hakki ba. Kungiyar ta kasashen larabawan ta hada kann alúmomin yankin ne domin samun masalaha ta warware rikicin kasar Iraqin wanda ke neman tabarbarewa zuwa yakin basasa.