´Yan siyasar Jamus sun yi lale maraba da babban taron Islama a Berlin | Zamantakewa | DW | 28.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

´Yan siyasar Jamus sun yi lale maraba da babban taron Islama a Berlin

Taron wani gagarumin mataki ne wajen kyautata zaman cude-ni in cude-ka tsakanin musulmi da Jamusawa a cikin wannan kasa.

Ministan cikin gida Wolfgang Schäuble

Ministan cikin gida Wolfgang Schäuble

Gabanin kaddamar da babban taron na Islama ministan harkokin cikin gidan na Jamus Wolfgang Schäuble ya sha suka da kakkausar harshe saboda rashin wani takamemen burin da taron yasa gaba da kuma zaben mahalarta taron. To amma a jawabin da ta yiwa majalisar dokoki ta Bundestag a yau shugabar jam´iyar adawa ta Greens Renate Künast ta yabawa matakain da mista Schäuble ya dauka.

“Ba tare da wata rufa-rufa ba, a madadin ´ya´yan jam´iyata a wannan majalisa, ina maraba tare da taya mista Schäuble murnar samun nasarar shirya wannan taro na Islama. Tun da dadewa mun bukaci daukar irin wannan mataki daga magabacinka.”

Kimanin shekara daya da ta gabata, magabacin nasa wato Otto Schily da kuma Künast sun kasance cikin majalisar ministocin tsohuwar gwamnatin kawance ta SPD da kuma The Greens. Künanst ta kuma yaba da kalaman da Schäuble ya yi amfani da su lokacin da yake gabatar da rahotonsa game da taron inda ya ce.

“Kamar yadda ya ke kunshe a cikin yarjejeniyar gwamnatin kawance, mun amince da tuntubar juna da dukkan al´umar musulmi a nan Jamus, wadanda a yanzu suka tashi daga matsayi na baki a cikinmu zuwa wani bangare na al´umar wannan kasa baki daya. Dole ne a fahimtar da al´ummar musulmin da wadanda ba musulmi ba a game da haka.”

Idan wadannan kalaman suka fito daga bakin wani minista dan jam´iyar CDU hakan na nufin ke nan an samu ci-gaba a cikin wannan al´uma, inji Renate Künast. Ta ce da kamata yayi a ce tuni an daina amfani da kalmar nan ta ake amfani da ita kan musulmin wato ´yan ci-rani da suka kakagida.

Duk da haka ´yar siyasar ta jam´iyar The Greens ta nuna shakkun cewa ko jam´iyun CDU da CSU sun samu wani ci-gaba na a zo a gani game da wannan batu. Ta ce ya zama wajibi a yi amfani da kalaman na Schäuble a matsayin wata madogara ta saukakawa bakin a nan kasar dokokin zama Jamusawa.

Shi ma wakilin jam´iyar ´yan canji kuma dan asalin kasar Turkiya Hkki Keskin ya bayyana samun takardun zama dan kasar ta Jamus a matsayin sharadin samun nasarar shirin kyautata zamantakewa cikin kasar.

“Kuskuren da ake yi shi ne dukkan shugabannin siyasa da wannan abin ya shafa na ganin samun takardun fasfo na Jamus shi ne mataki na karshe a shirye-shiryen kyautata zamantakewar tsakanin baki da Jamusawa.”

Ra´ayin dukkan jam´iyun ya zo daya cewa samun nasarar shigar da bakin a harkokin cikin kasar ya dogara ne da kwarewarsu a harshen Jamusanci. Dan jam´iyar adawa ta FDP Hartfried Wolf ya tofa albarkacin bakinsa ya na mai cewa.

“Duk wanda ya ki shiga cikin tattaunawar da ke yi yanzu a cikin al´umar kasar ko kuma da gangan ya kawo cikas ko hana wasu ba da gudunmawarsu to fa shi da kanshi ne ya mayar da kanshi saniyar ware.”

Wolf da sauran ´yan siyasar da suka yi jawabi sun nuna bukatar yin amfani da harshen jamusnci a cikin masallatai na kasar.
 • Kwanan wata 28.09.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTH
 • Kwanan wata 28.09.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvTH