Yan siyasa na Turai sunce Amurka ta canza akalarta | Labarai | DW | 10.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan siyasa na Turai sunce Amurka ta canza akalarta

Yan siyasa na kasashen turai sun ce suna sa ran kasar Amurka zata canza akalarta kann manufofinta na ketare,bayan kaye da jamiyar Bush ta sha a majalisun dokoki dana dattijai a zaben da aka gudanar ranar talata.

Elmar Brok,na majalisar dokokin Jamus yace yana ganin akwai yiwuwar cewa,gwamnatin Amurka zata canza dabarunta a Iraq da Afghanistan.

Yace yana fatar yan jamiyar demokrats zasu matsawa shugaba Bush lamba na ya janye wasu daga cikin dakarun Amurka dake Iraqi.

Tun farko kantoman dake kula da harkokin waje na Kungiyar Taraiyar Turai Javier Solana ya kira murabushin sakataren tsaron Amurka Rumsfeld cewa,alama ce dake nuna Washington tana canza dabarunta game da Iraqi.