´Yan sandan Zimbabwe sun yi awon gaba da ´yan adawa | Labarai | DW | 26.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan sandan Zimbabwe sun yi awon gaba da ´yan adawa

´Yan sanda a Zimbabwe sun kame magoya bayan ´yan adawa da jami´ai sama da 200 wadanda ke halartar wani taro a hedkwatar jam´iyar adawa ta Movement For Democratic Change, MDC a birnin Harare. Kakakin jam´iyar Nelson Chamisa ya fadawa kamfanin dillancin labarun Reuters cewa ´yan sanda sun kai samame a ofisoshin jam´iyar dake gidan Harvest ba tare da wata takardar izinin yin samame ba. Mista Chamisa ya ce samamen na daga cikin matakan tursasawa ´yan adawa da ake fuskanta a kasar ta Zimbabwe. Kungiyoyin adawa na zargin shugaba Robert Mugabe da take hakkin bil Adama tare da murkushe ´yan adawa. Shi kuwa a nasa bangare shugaba Mugabe na zargin ´yan adawa da kasashen yamma da kokarin tumbuke shi daga kan karagar mulkin kasar ta Zimbabwe mai fama da matsalolin tattalin arziki.