1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sandan Pakistan sun cafke wani matashi bisa zargi kisan Bhutto

January 19, 2008
https://p.dw.com/p/Cunz

A binciken da suke na gano wanda ya kashe shugabar ´yan adawar Pakistan Benazir Bhutto, ´yan sanda sun kame wani matashi. Majiyoyin jami´an tsaro sun ce mutumin yana cikin wani gungun mutane biyar wadanda shugaban masu tsattsauran ra´ayi na Pakistan Baitullah Mes´ud ya ba su kwangilar kashe misis Bhutto. Gwamnatin Pakistan dai na zargin magoya bayan ƙungiyar al-Qaida da hannu a kisan gillan da aka yiwa Bhutto a ranar 27 ga watan Disamba. To sai dai jam´iyar tsohuwar Firaministar ta nuna shakku ga wannan iƙirarin na gwamnati.