1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sandan Nijar biyu sun mutu a wani hari

Ramatu Garba Baba
January 24, 2018

Rahotanni daga jamhuriyar Nijar na cewa an kashe wasu 'yan sanda biyu tare da raunata wasu bakwai a wani hari da aka kai a kudu maso yammacin kasar.

https://p.dw.com/p/2rPPP
Nigeria - Soldaten an der Grenze zu Niger
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Babu karin bayani daga mahukuntan kasar kan harin da kuma sanin ko harin da aka ce an kai a wani kauye mai suna Kokoloukou da ke a yankin Tillaberie na ta'addanci ne a daren Litinin zuwa wayewar garin Talata.

Wani mazaunin kauyen ma ya tabbatar wa kamfanin yada labaran Faransa AFP faruwar lamarin.

A makon da ya gabata sojojin Nijar bakwai ne suka mutu a wani hari da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram da kaiwa. Sai dai kuma yankin da yake fama da ayyukan ta'addancin Boko Haram, a wasu lokuta ma da masu fashi da makami da kan yi garkuwa da manyan 'yan kasuwa don samun kudin fansa.