´Yan sandan Isra´ila sun fasa wata ƙungiyar matasa ´yan Nazi | Labarai | DW | 09.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan sandan Isra´ila sun fasa wata ƙungiyar matasa ´yan Nazi

´Yan sandan Isra´ila sun ce sun kame wasu matasa 8 ´yan asalin tsohuwar Tarayyar Sobiet wadanda ake zargi da tafiyar da wata kungiyar ´yan Nazi dake kai hare hare kan baki da masu kishin adinin Yahudu da masu shan kwaya da kuma marasa galihu. Kamun su dai ya kada al´umar wannan kasa wadda aka kafa ta shekaru 60 da suka wuce a matsayin wata mafaka ga Yahudawa bayan kisan kare dangi da ´yan Nazi Jamus suka yi musu. ´Yan sanda sun ce an kame matasan ne wata daya da ya wuce bayan an shafe tsawon shekara gudaana sa ido kansu. A cikin wani hoton bidiyo da suka harhada da kansu, matasan sun yi kwadawa marasa karfi duka hadda amfani da kwalaba akan wani sannan suna nuna biyayya ga Adolf Hitler ta hanyar yin wata gaisuwa ta ´yan Nazi. FM Isra´ila Ehud Olmert ya fusata da wannan bidiyo.