1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sandan Birtaniya zasu yiwa Mohammed Hanif tambayoyi a Australiya

July 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuH7
Hukumomin Australiya sun tsaurara matakan tsaro a fadin kasar baki daya gabanin isar wasu ´yan sandan Birtaniya wadanda zasu gudanar da bincike kan yunkurin dana bama-bamai a Londin da Scotland da bai yi nasara ba. Wata tawagar ´yan sandan Birtaniya karkashin jagorancin sifeton rundunar yaki da ta´addanci zasu taimaka wajen yiwa Mohammed Hanif mai shekaru 27 da haihuwa tambayoyi. A halin da ake ciki an tsawaita wa´adin ci-gaba da rike Hanif wanda likita ne a wani asibiti dake Australiya, a gidan wakafi har zuwa ranar juma´a, bisa wata bukata da hukumomin Australiya suka gabatar. Ya zuwa yanzu dai ba´a tuhumi Hanif ba wanda dan asalin kasar Indiya ne kuma a bara a Australiya ta dauke shi aiki daga Ingila.