´Yan sandan Birtaniya sun kai samame a birnin London | Labarai | DW | 02.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan sandan Birtaniya sun kai samame a birnin London

´Yan sandan Birtaniya sun harbe wani mutum har lahira sannan sun yiwa daya rauni a wani samamen yaki da ta´adanci da suka kai cikin wani gida dake birnin London. Wata sanarwar da ta bayar rundunar ´yan sandar Scotland Yard ta ce an harbe mutumin ne a wannan samame da aka kai da sanyin safiyar yau juma´a, bayan wasu bayanai na leken asiri da suka samu. Sanarwar ta ci-gaba da cewa ´yan sanda sama da 250 wasun su a cikin kayaki na kariya suka kutsa cikin gidan. Ko da yake ba´a ba da karin bayani ba, amma an ce samame bai da alaka da hare haren bam na kunar bakin wake da aka kai a birnin London a cikin watan yulin bara, inda mutane 52 suka halaka.