1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sandan bincike na Birtaniya sun isa Islamabad

January 4, 2008
https://p.dw.com/p/CkNC
´Yan sandan yaki da ta´addanci na hukumar ´yan sandan Birtaniya wato Scotland Yard sun isa a ƙasar Pakistan don taimakawa a binciken kisan gillan da aka yiwa shugabar ´yan adawa Benazir Bhutto. Shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya musanta zargin da aka yi cewa gwamnati na da hannu a kisan gillan yana mai cewa ba a ɓoye komai ba game da kisanta kuma an yi ta yiwa Bhutto gargaɗi game da barazanar sojojin sa kai na musulmi. Kisan gillan da aka yiwa Bhutto a makon jiya ya janyo fargaba dangane da tsaron lafiyar ´yan adawa waɗanda ke bukatar a inganta sha´anin tsaro gabanin zabukan da ake dage gudanawa har sai ranar 18 ga watan fabrairu.