1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun tarwatsa 'yan jarida da ke zanga zanga a ƙasar Kamaru

May 3, 2010

Jami'an tsaro sun yi amfani da kulake domin tarwatsa 'yan jarida da ke zanga zanga ranar 'yancin 'yan Jarida ta duniya

https://p.dw.com/p/NDS4
Hoto: AP

Jami'an tsaro a birnin Yawunde na ƙasar Kamaru sun tarwatsa wasu 'yan jarida da ke ƙoƙarin hallarta wani taron a wannan rana da aka ware ta kare 'yancin faɗar albarkacin bakin 'yan jarida.

'Yan jarida kimanin ɗari biyu ne zuwa ɗari ukku da ke kan hanyar zuwa fadar friminista Yang Philemon domin yin wani zaman durshin 'yan sandar suka tarwatsa su da kulake.

'Yan jarida dai na ƙasar ta Kamaru na fafatikar ganin gwamnati ta ƙaddamar da bincike akan mutuwar wani ɗan jaridar Germain Cyrille editan jaridar Cameroun Express da ya mutu a gidan kaso a ranar 22 ga watan Aprilun da ya gabata.

Ƙasar ta Kamaru dai na daga cikin ƙasashen da 'yan jarida suke kokawa da tursasawa da suke fama da ita ta jami'an gwamnati.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Mohamed Nasiru Awal