1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda sun tarwatsa 'yan adawa a Kongo

Salissou BoukariMay 13, 2016

A wannan Jumma'ar ce jami'an tsaron birnin Lubumbashi su ka yi amfani da karfi wajen tarwatsa dubban magoya bayan dan adawa Moïse Katumbi.

https://p.dw.com/p/1InVO
Symbolbild Polizei in Kinshasa
Hoto: Scoppa/AFP/Getty Images

'Yan sandan sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye a harabar kotun, yayin da a ciki kuma suka yi ta korar wasu tarin lauyoyi fiye da goma da suka zo kotun da zummar bada kariya kyauta ga dan adawan. Wannan rana dai ita ce ta uku da ake sauraron Katumbi, inda a wannan karon ma ya zo kotun ne ya na sanye da fararan kaya da wajejen karfe 12 agogon kasar tare da rakiyar lauyoyinsa da kuma iyalansa.

Shi dai tsohon gwamnan na Katanga Moise Katumbi ana aiwatar da bincike ne a kanshi kan batun amfani da wasu sojojin haya na kasashen waje ya sanar da aniyarsa a baya ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar ta Kongo da ta kamata ya gudana a karshen wannan shekara.