1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

`Yan sanda sun murkushe gangamin kyamar gwamnati a Dakar

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuTB

´Yan sanda a Senegal sun dauki tsauraran matakan murkushe wata zanga-zanga a Dakar babban birnin kasar. Rahotanni sun yi nuni da cewa an kame ´yan adawa 3 ´yan takara na zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa a ranar 25 ga watan fabrairu. Masu zanga-zangar na neman shugaban kasa Abdullahi Wade mai shekaru 80 da yayi murabus. Suna zarginsa da jefa abokan adawa a gidan kaso kana kuma yanan yawaita dage ranar gudanar da zaben ´yan majalisar dokoki. ´Yan sanda sun ce sun dauki wannan mataki ne domin ´yan adawa na gudanar da wata zanga-zanga ce da aka haramta saboda dalilai na tsaro.