′Yan sanda sun kashe dan Najeriya a Afrika ta Kudu | Labarai | DW | 06.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda sun kashe dan Najeriya a Afrika ta Kudu

Najeriya ta kira mai kula da harkokin kasa da kasa na Afirka ta Kudu da ke Abuja domin nuna bacin ranta kan yadda 'yan sanda suka yi sanadin mutuwar wani dan Najeriya a Afirka ta Kudu.

Südafrika Proteste Studenten Universität (Getty Images/AFP/M. Longari)

'Yan sandan Afrika ta Kudu

A wata sanarwa da ofishin ministan harkokin wajen kasar ta Najeriya ya fitar ta ce mutunen dan shekaru 27 da haihuwa mai suna Kingsley Ikeri, ya gamu da ajalinsa ne bayan da 'yan sandan  Afirka ta Kudu suka gana masa azaba a yankin Kwazulu-Natal, inda sanarwar ta ce 'yan sandan na tuhumarsa ne da fataucin miyagun kwayoyi.

Tuni dai karamar Ministar harkokin wajen ta Najeriya  Ifeoma Akabogu Chinwubab ta nuna bacin ranta ga wannan mataki na 'yan sandan kasar ta Afirka ta Kudu, inda ta nemi hukumomin kasar da su gurfanar da wadannan 'yan sanda a gaban kuliya ba tare da bata lokaci ba.