1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na neman Anis Amri kan harin Berlin

Zainab Mohammed Abubakar
December 21, 2016

Jami'an 'yan sanda a Jamus sun shiga farautar wani dan Tunusiya mai suna Anis Amri da ake zargi da hannunsa a harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin, wanda Kungiyar IS ta yi ikirarin daukar nauyi. 

https://p.dw.com/p/2Ugal
Fahndungsfoto Anis Amri
Hoto: picture-alliance/dpa/Bundeskriminalamt


Jami'an 'yan sanda a Tarayyar Jamus sun kaddamar da binciken wani da aka yi watsi da bukatunsa na neman mafaka Anis Amri, bisa zarginsa da hannu a mummunan harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin, wadda Kungiyar IS ta yi ikirarin daukar nauyi. 

Jami'ai sun shaidar da cewar an samu takardun ofishin neman mafakar siyasa mallakar matashin dan Tunisiya Anis Amri da ake zargi da alaka da Kungiyar IS a cikin motar da aka kai mummuna harin na Berlin wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutane 12, da kuma raunata wasu kusan 50, kamar yadda ministan kula da harkokin cikin gida na Jamus Thomas de Maiziere ya fada wa manema labaru.

" Akwai wani da ake zargi. Ana cigaba da gudanar da bincike. Kamar kowa, ina magana ne a kan zargi, amma ba wai lallai shi ne ya aikata laifin ba. Za'a ci gaba da bincike ta kowane bangare. Muna bin diddigi. Kuma tuni aka gabatar da takardar izinin kama wanda ake zargin, a nan Jamus da kasashen Schengen da ma Turai baki daya".

Deutschland Berlin - Polizeiwache an der Kaisser-Wilhelm-Gedächtniskirche
Hoto: Getty Images/AFP/C. Bilan

Sai dai ministan cikin gida na jihar North Rhine-Westphalia Ralf Jaeger ya ce mutumin da ake nema ruwa a jallo wanda aka sani ta kafofin yada labaru da suna Anis Amri an dade ana gudanar da bincike a kansa saboda shirya kai hari. A baya bayannan kwararru a fannin ta'addanci sun yi musayar bayanai tare da kaddamar da bincike a kansa a watan Nuwamba kan zargin shirin kai munanan hari a cikin kasar.

Mutumin da ake zargin Anis Amri ya zo Jamus ne a watan Yulin shekarata ta 2015 da ta gabata. A watan Yuni ne kuma aka yi watsi da bukatunsa na neman izinin zama a kasar. Sai dai an gaza korarsa daga kasar, wadda tuni ta ce ba dan kasar ba ne.


Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa na Italiya Angelino Alfano sun ziyarci mujami'ar da ke kusa da wurin harin na daren Litinin, inda kuma nan ne ake makoki tare da bude littafin sakonnin ta'aziyya domin jimamin wadanda harin ya ritsa da su. Steinmeier ya lashi takobin cewar, babu wanda ya isa ya bata salon rayuwar Jamusawa.

" Muna farin cikin sanin cewar akwai mutanen da ke tare da mu a wannan yanayi na bakin ciki da juyayi da muke ciki. Hakan na nufin za mu iya dogaro da abokanmu na Turai da sauran kasashen duniya. Mun samu sakonnin ta'aziyya da na goyon baya masu yawa a 'yan kwanakin da suka gabata".

Deutschland LKW nach dem Anschlag am Breitscheidplatz in Berlin
Hoto: Reuters/H. Hanschke

Tuni dai gwamnatin Jamus ta amince da wata doka da za ta karfafa tsaro da ta danganci kamarorin bidiyo na tsaro da ake sanyawa a wuraren jama'a. Steffen Seibert  shi ne mai magana da yawun gwamnatin Jamus...

" Za'a amince da dokokin da suka danganci kamarori na musamman da ake sawa saboda tsaro, ta yadda ba zai shafi rayuwar mutane ko walwala da kuma lafiyarsu ba".

Yanzu haka dai gwamnatin Jamus ta sanar da cewa za ta bada tukwicin euro dubu 100 ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga cafke wadanda ke da hannu a harin na Berlin.