Yan sanda na cin zarafin jamaá a Niger | Labarai | DW | 27.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan sanda na cin zarafin jamaá a Niger

Kungiyar kula da hakkin bil Adama ta jamhuriyar Niger ta ce har yanzu ana samun rahotannin azabtarwa da yan sanda ke yiwa jamaá a chaji Ofis. Kungiyar tace wajibi ne mahukunta su tsawatar domin dakatar da wannan mummunan dabiá. Shugaban hukumar kare hakkin bil Adaman ta Niger Garba Lompo ya yi nuni da cewa Niger na daga cikin kasashe wadanda suka sanya hannu a kan kudirin kasa da kasa a shekara ta 2003 da ya yi hani ga azabtar da jamaá. Hukumar kare hakkin bil Adaman ta kuma yi kira ga dukkanin jamiái su martaba daurarru dake tsare a gidajen kurkuku tare da basu hakkin su kamar yadda ya dace. A watan da ya gabata wani wanda ake tsare da shi a ofishin yan sanda a birnin Yamai ya rasa ran sa abin da kungiyar hakkin bil Adama ta ANDDH ta baiyana da cewa ya rahoton bincike ya nuna ya rasu ne sakamakon azbtarwa da ya sha a hannun yan sandan.