1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan sanda na ci gaba da yin bincike a Turkiyya

January 2, 2017

Har ya zuwa yanzu 'yan sanda ba su kama wanda ya kai harin birnin Istanbul ba,sai dai rahotannin na cewar an tsare wasu mutane guda takwas ana yi musu tambayoyi a game da harin.

https://p.dw.com/p/2V9NE
Türkei Anschlag Nachtklub
Hoto: Reuters/O.Orsal

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin da wani dan bindiga ya kai a wani gidan rawa a birnin Istanbul na Turkiyya a lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekara; wanda a ciki mutane 39 suka mutu kana wasu da dama suka rasa rayukansu.A cikin wata sanarwa da kungiyar ta baiyana a shafukanta na  sada zumunta ta ce sojinta ne ya kai harin.