′Yan sanda na ci gaba da yin bincike a St. Petersburg | Labarai | DW | 04.04.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan sanda na ci gaba da yin bincike a St. Petersburg

Ana hasashen cewar wanda ya kai harin da mutane 11 suka mutu kana 50 suka jikka dan yankin tsakiya ne na Asiya.

Majiyoyin yada labarai na Rasha na cewar mutumin da ake zargin da kai tagwayen hare-hare na kunar bakin wake a tashar jiragen kasa ta birnin St. Petersburg  yana da kimanin shekaru 23 da haifuwa kuma dan asilin yankin Asiya ne ta tsakiyya ne.Ko da shi ke har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da wannan labari, ba amma dai, masu aiko da rahotannin sun ce  gwaje-gwaje na  jini na kwayoyin halitu kawai zai iya tantance wanda ke da alhakin harin.Mutane guda 11 suka kana wasu 50 suka jikkata bayan da bam  ta tawartse a cikin tashar wadda bayyanai suka nuna cewar an nadeta a cijkin jikar da ake ratayawa a baya.

i