Yan sanda a Masar sun kame wasu Turawa da yunkurin aikata harin taáddanci | Labarai | DW | 04.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan sanda a Masar sun kame wasu Turawa da yunkurin aikata harin taáddanci

Yan sanda a Masar sun cafke wani ba Amurke daya da turawa goma sha daya tare kuma da wasu mutane da dama daga kasashen larabawa da yunkurin aikata hare haren taáddanci a kasashen gabas ta tsakiya ciki har da kasar Iraqi. A cikin wata sanarwa, maíakatar alámuran cikin gida ta kasar Masar ta ce gungun mutanen reshe ne na wata kungiya ta yan takifen muslmi da suka dauki akida ta tsatsauran raáyi da kuma suke zaune a Masar da togaciyar cewa suna nazarin harshen larabci ne ko kuma suna karatu da ya shafi addinin musulunci.Baya ga Ba Amurken yan sanda sun kuma cafke wasu yan kasar Belgium biyu da faransawa tara da wasu mutanen da dama daga kasashen Masar da Tuinisia da kuma Syria. Dukkanin mutanen ana tsare da su a gidan yari kafin cigaba da gudanar da bincike.