1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sanda a Lyon sun yi amfani da barkonon tsohuwa kan masu tarzoma

November 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvLN

Hukumomin kasar Faransa sun ce an bankawa motoci wuta a birane Toulouse da Lyon a dare na 17 na ci-gaba da tarzoma da tashe tashen hankula a fadin kasar. Ba wani rahoton wani tashin hankali a Paris, inda aka girke dubban ´yan sanda don tinkarar duk wani hargitsi da ka iya barkewa a karshen mako. Har izuwa safiyar yau lahadi an haramta yin tarurruka da ka iya janyo wata rigima a kasar. Sannan a karshen wannan mako hukumomin sun kafa dokar hana fitar dare a garuruwa 10 dake kudu maso gabashin kasar ta Faransa, sannan a hana yara da matasa fita ba tare da iyayensu ko wani babba da su ba. A Lyon birni na 3 mafi girma a Faransa ´yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa gungun mutane dake jifa da duwatsu gabanin dokar hana fitar ta fara aiki.