1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sanda a London na farautar masu hannu a yunkurin kai harin bam

June 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuHa
Ana ci-gaba da farautar mutanen da ke da hannu a yunkurin kai hare haren bama-bamai da motoci biyu a tsakiyar birnin London wanda bai yi nasara ba. ´Yan sandan ciki na gudanar da bincike a wasu fayafayen bidiyo da fatan gano direbobin motocin guda biya. A kuma halin da ake ciki wani tsohon kwamandan rundunar ´yan sandan Scotland Yard ya ce hukumomi zasu yi amfani da abin da ya kira bayanai masu alfanu da shaidar da aka bari a cikin motoci da ba su yi bindiga ba. Kawo yanzu abin da aka gano dangane da motocin shi ne suna da alaka inji shugaban hukumar ´yan sandan yaki da ta´addanci a birnin London Peter Clarke. Ministar cikin gida Jacqui Smith ta yi kira ga jama´a da su kasance masu lura da abubuwan da ka je su komo. Yunkurin kai harin ya zo kwanaki biyu bayan da Gordon Brown ya dare kan kujerar FM Birtaniya.