1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan sanda a Londom sun yi babban kamu

December 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvFd

Yan sandan kundunbala a birnin London sun cafke wani mutum guda da suke zargi nada hannu a cikin harin nan da aka kai birnin Londonm a watan yuli na wannan shekara.

Rahotanni sun shaidar da cewa yan sandan sun cafke mutumin ne jim kadan da saukar sa daga jirgin sama a filin jirgin sama na Gatwick daga kasar Habasha.

Idan dai za a iya tunawa an cafke wasu mutane hudu da suka yi kokarin tashin wasu bama baman a karkashin tashar jiragen kasa a birnin amma hakan bai samu cimma nasara ba.