1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

´Yan sanda a Biratniya na ci-gaba da neman masu hannu a shirin tarwatsa jiragen sama

August 11, 2006
https://p.dw.com/p/Bun3
An tsaurara matakan tsaro a dukkan filayen jiragen sama a fadin duniya baki daya bayan da hukumomin Birtaniya suka bankado wani makircin tarwatsa jiragen sama kimanin guda 10 wadanda zasu tashi daga Birtaniya zuwa Amirka. A Birtaniya kanta har yanzu ana cikin zaman shirin ko-takwana yayin da ´yan sanda ke ci-gaba da neman karin mutane da aka yi imani suna da hannu a wannan shiri na kai hare haren. Kawo yanzu an kama mutane 24 dukkansu musulmi ´yan Birtaniya a biranen London da Birmingham yayin da kuma babban bankin Ingila ya dora hannun kan takardun ajiyar kudi na mutum 19 a cikinsu tare da bayyana sunayensu. Hukumomi a Birtaniya sun yi imani cewa wadanda ake zargin sun so su yi sumogan wasu bama-bamai ne na ruwa ruwa cikin jiragen sama wadanda zasu harhada su a cikin jirgin. Jami´ai sun ce maharan sun yi shirin aikata abin da suka kira kisan kare dangi. Pakistan ta ce jami´an leken asirinta sun taimaka wajen dakatar da wannan makarkashiya kana ita ma ta kama mutane da dama. Ana sa rai a yau ma za´a fuskanci cikas a harkokin zirga zirgar jiragen sama.