Yan sanda a ƙasar jamus sun dakatar da mutane sama da ɗari biyar | Labarai | DW | 02.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan sanda a ƙasar jamus sun dakatar da mutane sama da ɗari biyar

Yan sanda sun dakatar da mutane 500 a garuruwan Berlin da Hamburg bayan bikin sallah maikata

default

Yan sanda a birnin Berlin na kama masu zanga zanga

sama da mutane 500 ne  hukumar yan sanda ta nan ƙasar jamus ta dakatar a garuruwan Berlin dakuma Hambourg, a ƙarshen wannan mako,bayan bikin sallah maikata wanda wasu masu zanga zangar da ke da tsatsaura ra'ayi suka yi amfanin da damar domin tayar da borai.

Masu zanga zangar galibi matasa sun abkawa kantina da bankuna wanda suka hadasa asara ga shaguna 15 a daren asabar zuwa lahadi.

Shugaban hukumar yan sanda na garin Berlin Dieter Glietsch, wanda ya ce sun baza jami'an tsaro  kimanin 7300 ya sheda cewa batare da ɓata lokaci ba, sun murƙushe boren,to sai dai ya ce an samu yan sanda kamar 85 da suka samu rauni  a sakamakon jifa da butala dakuma duwatsu da masu zanga zangar suka rika yi

Wani Senata a birnin na Berlin  Ehrhat Körting ya jinjinama yan sandar.

Ina tsamanin wannan yunƙuri ya na  da mahimanci a garemu da kuma birnin  dangane da yadda waɗanan jami'an tsaro suka  kwantar da tarzoma ,inda aka yi misali da shekara bara a dadai wannan lokaci irin ta'adin da aka samu za iya cewa a wannan shekara yan sanda sun yi nasara hana tayar da fitina .

Mawallafi :Abdourahamane Hassane

Edita        : Abdullahi   Tanko  Bala