1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Najeriya za su kalubalanci Shell a Holand

Mai shari'a Hans van der Klooster ya ce kotun daukaka karar da ke a birnin Hague na da hurumi na sauraran wannan shari'a.

Umweltverschmutzung im Niger Delta

Yankin da hakar ma'adanai ta gurbata a Niger Delta-Najeriya

Wata kotun daukaka kara a kasar Holand ta bayyana a ranar Juma'an nan cewa wasu manoma hudu 'yan Najeriya na da dama a kasar su daukaka karar da suke yi ta kamfanin hakar albarkatun man fetir wato Shell cewa ya bata musu muhalli a Najeriya. Wannan hukunci dai na zama wanda ya kafa tarihi da aka samu hannun kamfanin na Shell a irin wannan shari'a.

Mai shari'a Hans van der Klooster ya ce kotun daukaka karar da ke a birnin Hague na da hurumi na sauraran wannan shari'a kan kamfanin da ke da reshe a Najeriya.

Manoman hudu da masunta daga yankin Niger Delta a Najeriya sun sami goyon baya ne na wata kungiya mai fafutikar kare muhalli mai suna Freands of the Earth wacce tun a shekarar 2008 ta gurfanar da wannan kamfani a kotun da ke da tazarar dubban kilomitoci daga inda lamarin gurbata muhallin ya faru.