Yan Najeriya na auren Visa don shiga Turai | Labarai | DW | 12.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Najeriya na auren Visa don shiga Turai

'Yan sandan Jamus sun kai samame kan wasu gungun yan Najeriya a Berlin bisa zambar shirya auren Visa domin shiga kasashen Turai cikin sauki

'Yan sandan Jamus da na Portugal sun kai samame gidajen wasu gungun mutane da ake zargi da shirya auren Visa yawancinsu yan Najeriya domin samun damar zuwa Turai cikin sauki.

Rundunar yan sanda a Berlin ta ce an kai samame gidaje 41 da ofisoshi an kuma kama mutane biyar.

Jami'an sun kwace fasfuna da takardun zama yan kasashen Turai da wayoyin salula da kuma wasu na'urori.

Haka ma dai hukumomi a Portugal sun kai irin wannan farmaki a lokaci guda.

Kakakin rundunar yan sandan Jamus Jens Schobranski yace daga cikin wadanda ake zargi da aka tsare sun hada da wani dan Najeriya mai shekaru 50 da kuma wasu mata biyu Jamusawa yan shekaru 55 da kuma 64.

Ana zargin su da sayar da satifiket ga maza yan Najeriya domin shirya auren bogi da matan Portugal.

Rundunar yan sandan ta ce ta gano an gudanar da irin wannan auren Visa har guda 70 yayin da mutanen suke karbar tsabar kudi euro dubu 13 a kowane aure.