1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: 'Yan matan Dapchi sun samu 'yanci

March 21, 2018

Kungiyar Boko Haram ta sako dalibai ‘yan mata 'yan makarantar sekandaren kimiyya na garin Dapchi cikin karamar hukumar Bursari da ke jihar Yobe bayan kwashe kwanaki 30 a hannun kungiyar.

https://p.dw.com/p/2uhN5
Boko Haram lässt entführte Mädchen frei
'Yan matan sakandaren Dapchi da Boko Haram ta dawo da suHoto: Reuters/O. Lanre

Bayan da mayakan Boko Haram cikin ayarin motocinsu suka shiga garin da misalin karfe 7:45 na safiya suka kuma ajiye daliban da suka sace makwanni uku da suka gabata, garin na Dapchi da ke karamar hukumar Bursari ya kasance cikin yanayi na murna. Garin ya rude ko in aka shiga ana murna inda bayan isar 'yan matan gidajensu al'umma suka yi ta yin tururuwa suna zuwa domin taya iyaye da kuma 'yan matan barka. Yanzu haka dai jami'an tsaro na kan tattara daliban zuwa babban asibitin garin Dapchi domin duba lafiyarsu inda jami'an tsaron suka killace asibitin tare da hana iyaye da manema labarai shiga domin ganawa da sauran daliban.

Kusan dukka daliban 104 suka dawo ga iyayen inda bayanai ke cewa guda biyar sun mutu a hanyar tafiya da su yayinda mayakan suka rike guda daya daga cikin ‘yan matan. Alh Inuwa Garba Bayamari na cikin iyayen da ba su ga 'ya'yansu ba, inda ya shaida cikin jimami da damuwa cewa 'yan matan da suka dawo sun shaida masa cewa ta rasu yayin da su ke tafiya. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mayakan da yawancin su suka rufe fuskokinsu sun ajiye daliban a bakin tashar garin, inda kuma su ka yi musu takaitaccen bayani kafin su fice su koma inda su ka fito.