1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan matan Chibok za su koma gida

August 19, 2017

Mahukunta a Najeriya, sun ce sama da 'yan matan makarantar Chibok 100 da suka kubuta daga hannun Boko Haram na gab da komawa gida su ci gaba da harkokinsu na rayuwa yadda suka saba a baya.

https://p.dw.com/p/2iUf1
Nigeria - Heimkehr der Chibok Mädchen
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Gwamnatin Najeriya, ta ce sama da 'yan matan makarantar Chibok 100 da suka kubuta daga hannun Boko Haram din nan, suna gab da komawa harkokinsu na rayuwa yadda suka saba a baya. Ministar harkokin mata ta Najeriyar ce ta sanar da hakan a wata ganawar da ta yi da manema labarai, tana mai tabbatar da cewa 'yan matan su 106 sun warke tsaf, kuma za su mika su da iyayensu, su kuma koma makaranta.

Su dai wadannan 'yan mata na Chibok sun sami kulawa ta musamman a hannun mahukuntan Abuja, bayan sako su da mayakan Boko Haram suka yi. Cikin watan Mayun bana ne kungiyar ta Boko Haram ta sako 82, wasu 24 ma suka kubuta a bara. Bayan 'yan matan na Chibok kimanin 100 suka saura yanzu a hannun Boko Haram, akwai ma wasu daruruwan jama'a mata da maza da kungiyar ke garkuwa da su.