1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yan majalisar dottijan Amurka sun kada kuriu

March 29, 2007
https://p.dw.com/p/BuOo

Yan majalisar dottijai na Amurka sun kada kuriar amincewa da kudurin dake bukatar fadar gwamnati ta white house ta janye dakarunta dake Iraki nan da watan maris na shekarat 2008,adangane da karin kudi data nema na cigaba da daukan nauyin rigingimu dake gudana a Irakin da kuma Af´ganistan.Majalisar ta cimma wannan kuduri ne inda wakilai 51 suka kada kuriunsu na amincewa da janye dakarun kana,wasu 47 suka nuna adawa,adangane da kudaden da ake kashwa wanda ya kunshi dala billion 122.Gabannin kada kuriun dai Bush ya gana da yan majalisar dokoki daga jammiiyarsa ta Republican,inda ya nemi goyon bayansu a wannan kuduri nasa.