Yan majalisar Dottijai sun amince da dokar haramta shantaba | Labarai | DW | 06.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan majalisar Dottijai sun amince da dokar haramta shantaba

Majalisar dojjijai ta tarayyar Jamus ta amince da rage kudaden harajin wa kamfanoni ,kama daga watan janairun shekara mai zuwa.kudaden haraji da gwamnatin take samu daga kamfanoni zai rage daga kashi 39 daga cikin 100,zuwa kashi 30.Majalisar dottijan ta Bundesrat wadda ke wakiltar jihohin kasar 16,ta kuma amince da dokar haramta shan taba a cikin motoci da jirage na pasinja,da maaikatun gwamnatin tarayya guda 500.Wannan dokar haramta shan taba a wadannan wurare dai zata fara aiki ne daga watan Satumba.