1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan majalisar dokokin Yukren sun baiwa hamattan juna iska

April 27, 2010

Majalisar dokokin Yukren ta kasance fagen doke - doke a yau Talata.

https://p.dw.com/p/N8CF
Yanukovich a ɓangaren dama, da kuma Frime ministan ƙasarHoto: AP

Zauren taron majalisar dokokin ƙasar Yukren ya kasance dandalin dambe a yau Talata, inda baya ga doke doken da 'yan majalisar suka yiwa junan su, sun kuma ta yin jifa da ƙwayaye a yayin da 'yan adawa a majalisar suka nuna fushin su game da wata yarjejeniyar da gwamnatin ƙasar ta cimma tare da ƙasar Rasha wadda ta tanadi mayaƙan Rasha su ci gaba da yin amfani da sansanin sojin ruwa a Yukren. Sai dai duk da bata kashin, 'yan majalisar, waɗanda galibin su daga ƙawancen jam'iyyun da suka kafa mulki tare da shugaban ƙasar Viktor Yanukovich, sun amince da tsawaita wa'adin shekaru 25 ga kasancewar mayaƙan ruwar Rashar a sansanin Crimea dake kan kogin Bahrul Aswad.

A makon jiya ne dai shugaba Yanukovich ya cimma yarjejeniyar tare da takwaran aikin sa na Rasha Dmitry Medvedev, inda Rasha zata sa'kawa Yukren da ragin kashi 30 cikin 100 na farashin iskar gas da take sayar mata. Dubbannin magoya bayan tsohuwar gwamnatin Yukren, wadda ke da ra'ayin ɗa'sawa da ƙasashen yamma ne dai suka yi jerin gwano a wajen majalisar dokokin domin nuna fushin su ga yanke wannan shawarar.