Yan majalisa a ukraine sunyi watsi da batun rushe majalisar | Labarai | DW | 03.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan majalisa a ukraine sunyi watsi da batun rushe majalisar

Membobin majalisar dokokin kasar Ukraine sun lashi takobin ci gaba da zama duk kuwa da dokar da shugaba Victor Yushchenko yayi na rushe majalisar da kiran zabe .

Wani kudiri da yan majalisar suka amince a kai a wani taron gagagwa da suka kira ya baiyana wannan doka a matsayin wani mataki na yunkurin juyin mulki.

Yan majalisar sun kuma jefa kuria ta kin amince da daukar nauyin gudanar da zaben,sun kuma amince da rushe hukumar zabe ta kasar

Wannan kuwa yazo ne saoi kadan bayan shugaban kasar ta Ukraine ya sanarda da shirinsa na rushe majalisar tare da saka ranar 27 ga watan mayu ranar zabe a kasar.

Yushchenko mai samun goyon bayan kasashen yammam ya zargi firaminista dake da goyon Rasha da laifin nema kara fadada ikonsa yana mai karya dokokin tsarin mulkin kasar.