1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

'Yan Kwango sun ba da tallafin kudi ga 'yan gudun hijira a Jamus

Wata majami'a daga garin Goma na Kwango ta yi wani abin al'ajabi a Jamus, inda ta ba da tallafin kudi ga 'yan gudun hijira a Jamus, duk kuwa da matsalolin da su kansu suke fuskanta.

Evangelischer Kirchenkreis Saar-West Kirchenkreis Ostkongo

Hulda tsakanin Cocin na gabashin Kwango da jihar Saarland ta kai shekaru 30

Sau tari dai daga kasashen yammacin duniya da kuma na Turai kungiyoyi da sauran hukumomi kan bada tallafin kudade domin taimaka wa al'umma sakamakon bala'i da hadarukan da a kan samu galibi a kasashen Afirka. To amma a nan labarin ya sha bambam, domin kuwa wata tawagar jami'an cocin Baptist ne na garin Goma da ke a Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta bada tallafin kudi na dala dubu daya ga wata majami'ar Evangelika da ke a Saarland wata karamar jiha da ke a yammacin Jamus don taimaka wa mata 'yan gudun hijira.

Evangelischer Kirchenkreis Saar-West Kirchenkreis Ostkongo

Kambale Kilumbiro Martin na mika kyautar kudin daga Kwango

Dala dubbun dai wanda aka saka a cikin ambula na zaman kudade masu yawan gaske a Jamuhriyar ta Demokradiyyar Kwango, kasar da ke fama da yakin basasa na tsawon shekaru da dama, abinda ya tilasta wa wasu dubban mutane yin gudun hjira a cikin kasarsu.

Taimakon juna a lokutan bala'o'i

Kambale Kilumbiro wanda ke kula da harkokin kudi na cocin da ke a garin Goma wanda shi ya mika kyautar ga jihar ta Saarland, ya ce jihar ta saba taimaka musu, don haka su ma suka ga ya kamata su taimaka mata a dawainiyar da take dauka ta 'yan gudun hijira, kana kuma ya ce karfin hali ne suka yi.

"Gaskiya ne muna cikin wani mawuyacin hali a kasarmu, to amma da yake muna da hulda da 'yan uwa na jihar Saarland ta Jamus wadanda su ma sukan bamu gundunmawa idan muna cikin matsala, don haka muka ga cewar ba za mu iya yin shiru ba."

Sama da shekaru 30 ke nan da ake yin hulda tsakanin cocin na Baptist na garin Goma da kuma cocin Evangelika na Saarland. Kuma domin kaddamar da bukukuwan tuna wa da zagayowar cikon shekarun, wata tawagar ta cocin na Evagelika ta iso a nan kasar Jamus a farko wannan wata.

Evangelischer Kirchenkreis Saar-West Kirchenkreis Ostkongo

Tawagar Kwango a ziyarar da ta kai a wani sansanin 'yan gudun hijira da ke Lebach, Saarland

Kafin a gudanar da bikin ba da tallafin kudin daga garin Goma, wani jami'in cocin a Saarland, Christian Weyer, ya ce wannan kyauta ta kudin da aka basu na jaddada abotakar da ke tsakaninsu.

"Mun saba taimaka wa Kwango sosai kuma akwai bukatar taimakawa a yankin na arewacin Kwango, saboda ina kallon wannan kyauta ko wannan yunkuri da cewar wani abun mutunci ne da abokananmu suka kawo mana. A shirye muke har kullum mu taimaka musu kuma mun yi farin ciki, sai dai kuma na ji 'yar kunya."

A shekarar 2002 Jamus ta taimaka wa Kwango bayan afkuwar wani mummunar bala'i da aka samu na wani rafin da ya rika yin aman wuta a yankin kudu maso gabashin kasar inda Jamus ta sake gina makarantu da asibitoci da kuma samar da ruwan sha na famfo a yankin.

Wannan tallafi dai da cocin Baptist din na Goma ya bayar za a yi amfani da shi wajen taimaka wa mata 'yan gudun hijira wadanda cocin Evagelika na Saarland ke daukar dawainiyarsu. Abigael Kavugho da ke zama daya daga cikin shugabannin cocin Baptist a Goma ta ce idan akwai bala'i mata suka fi shan wahala.