Yan kungiyyar Mossob sunyi arangama da yan sanda a Nigeria | Labarai | DW | 06.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan kungiyyar Mossob sunyi arangama da yan sanda a Nigeria

Yan kungiyyar Mossob dake kokarin ballewa daga Nigeria don kafa kasar Biafra, sunyi arangama da jami´an yan sanda a garin Onitsha, wanda hakan yayi sanadiyyar ajalin mutane uku.

Wannan dai arangama a cewar wani daya ganewa idon sa ta afku ne a yayin da yan kungiyyar ke kone konen tayoyi bisa manufar rurrufe hanyoyi don tsayar da harkokin sufuri.

Idan dai za a iya tunawa kungiyyar ta Mossob ta bukaci kabilar Igbo dasu kasance a gida a ranakun biyar da shida ga wata , wanda hakan ke matsayin nuna rashin amincewar ci gaba da tsare shugaban kungiyyar ta Mossob da rundunar yan sandan kasar keyi.

Ya zuwa yanzu dai mahukuntan na Nigeria sun tabbatar da cewa wannanm yunkuri na kungiyyar ta Mossob cin amanar kasa ce a don haka an cafke da yawa daga cikin yan kungiyyar.

Idan dai za a iya tunawa a lokacin yakin basasa daya faru na kokarin kafa kasar ta Biafra, yan kabilar ta Igbo sama da miliyan daya ne suka rasa rayukan su a sabili da wahala da kuma yunwa.