1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan kunar bakin wake sunyi kurarin kai wasu sabbin hare hare

Wani dan kunar bakin wake da aka nuno sh a gidan talabijin na kasar Indonesia ya gargadi kasashen yamma dasu kwana da shirin su domin nan bada dadewa ba za a kawo musu hare hare na kunar bakin wake.

A cewar rahotanni daga kasar an tsinto wannan bidiyon da aka sa ne a yankin da ake zargi na tsageru masu tsattsauran raayi ne a wannan kasa, a yayin da yan sanda ke gudanar da sintiri a wannan yanki.

Mutumin ,wanda gidan talabijin din kasar ya nuno shi fuskar sa a rufe yayi kurarin cewa kasashen da wannan abu zai shafa sun hadar da Amurka da Biritaniya da Australia da kuma Italiya, wanda yace makiya addinin musulunci ne.

Ya zuwa yanzu dai tuni jamian yan sanda suka ce suna zargin wannan mutumi ba zai wuce Nuruddin Mohd ba, mutumin da suke zargi shugaban kungiyyar Alqeda ne dake kula da kudu maso gabashin yankin Asia.