′Yan Kataloniya sun ja daga da ′yansanda | Labarai | DW | 30.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan Kataloniya sun ja daga da 'yansanda

Duk da baza jami'an tsrao da aka yi a harabar gudanar da zaben, daruruwan al'ummar Kataloniya sun gudanar da gangami daban daban a yau Asabar, da nufin nuna jajircewarsu na kada kuri'un neman 'yanci a gobe Lahadi.

Wannan dai wani mataki ne da 'yan yankin na Kataloniya suka dauka na yin zaman dirshen a cibiyoyin zaben, da zai hana jami'an tsaro killace harabar makarantun da ake sa ran gudanar da zaben. To sai dai tun ba yau ba kotun kundin tsarin mulkin Madrid ta haramta yunkurin zaben.

Shugaban Kataloniya Carles Puigdemont, ya jadda da manufar su ta ba gudu ba ja da baya a dangane da kada kuri'ar neman 'yancin a gobe kamar yadda suka shirya, inda ya ke cewa:

"Mun samu nasara kan fargaba da duk wata barazana. Mun samu nasara kan matsin lamba da tursasawa, mun cimma nasara kan gwamnatin danniya, wadda bata muradin mu kai wannan matsayin. Bata muradin mu aitawatar da wannan mataki cikin lumana, kasancewar basu san mu ba, sun yi zata zamu janye, ba su san suna bamu kwarin gwiwa ba ne."

 

Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Spaniya ya sahidar da cewar jami'an 'yan sanda sun mamaye cibiyar sadarwar da ke kula da yankin, kuma zasu kasance a wurin na tsawon kwanaki biyu. Wannan dai na bangaren umarnin da babban kotun Kataloniyan ta bayar a ranar Juma'a, domin hana kada kuri'ar.