Yan kasuwan jamus a Sudan | Zamantakewa | DW | 27.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Yan kasuwan jamus a Sudan

Ire iren rawa da yan kasuwan jamus ke takawa wajen bunkasa Sudan

Kudancin Sudan

Kudancin Sudan

Yan majalisar dokoki na tarayyar jamus sun kada kuriar amincewa da fadada waadin dakarun kasar kalilan dake lardin Darfur din kasar Sudan,da karin watanni shida.To ko yaya dangantakar jamusawa da kasar ta Sudan bisa laakari da ayyukanta a wannan kasa.

Yankin yammacin kasar ta sudan dai nacigaba da fuskantar tashe tashen hankula tsakanin yan tawaye da kuma mayaka dake marawa gwamnatin khartum baya,ayayinda sauran yankunan kasar ake cigaba da dibar albarkatun zinari.Ana dai samun bunkasar tattalin arziki a yankunan arewaci da kuma kudancin kasar.

Kasar Sin dai ta mayar da hankali wajen cin moriyar albarkatun mai na wannan kasa,ayayin da Amurka a nata bangare ta mayar da hankali ta fannin makamashi,kana jamusawa ke cigaba da bunkasa harkokin masanantu a wannan kasa.

Masaantar safarar naurar gine gine dana ababan hawa zuwa kasashen ketare dake birnin Hamburg anan jamus ,na taka rawa a kasar sudan.Sudan din dai itace suke huldodin harkokin mai da manyan tankunan samarda da ruwansha da naurorin buga jaridu,wadanda yan kasuwa na jamus din ke samar mata.

A wannan kasa dake yankin tsakiyar Afrika dai ,wannan masanaanta tayi shekaru 53 tana tasiri cikin harkokin cinikayyanta.Bayan yakin basasa daya gudana a kudancin Sudan ,da kuma tsawon shekaru na nunawa yankunan wariya,ayanzu haka akwai bukatar mayar da hankali wajen bunkasa cigabanta,kamar yadda manajan ciniki na kamfanin Cramm & Co ya bayyana...

“ A kasa kamar Sudan ana bukatar hadin kai tsakanin alummominta,kamar yadda ake muradin hadewanta cikin harkoki na tafiyar da rayuwa a da sauran kasashen duniya,musamman ta fannin cigaban tattalin arziki.A kudancin Sudan din dai babu wani abun azo a gani ta fannin cigaba.Domin a yanzu haka babu Bankuna ,babu kayayakin more rayuwa ,kana babu ingantattun titunan ababan hawa.Adangane da hakane yankin yake bukatar kyakkyawar kulawa,domin rayuwar alummominsu”

Wannan masanaanta ta Hamburg dai ba ita kadaice ke wakiltar jamus din a Sudan ba.A watannin baya da suka gabata maaikatar kula da harkokin tattali da fasaha dake tarayyar jamus da takwararsu ta Afrika,sun gudanar da wani rangadin gani da ido a yankunan Arewaci da kuidancin sudan din,tawagar data kunshi yan kasuwan nan jamus guda 28.

To sai rigingimu dake cigaba da addabar Lardin Darfur dake yammacin kasar da kuma saniyar ware da gwamnatin Sudan din ta mayar da yankin,na ciga da haifar da tsako a kokarin bunkasuwarsa.

Philip Müller,manazarcin harkokin kasuwanci ne a jamus...

“A dangane da halinda ake ciki a lardin Darfur babu wata tattaunsawa da zaayi,saboda gwamnati kasar nada angizo acikin rikicin ,kazalika dukkan wakilai na wannan gwamnati”

Ana cigaba da fuskantar matsaloli na take hakkin biladama dai a kasar ta Sudan.Sai dai yan kasuwan na jamus na cigaba da taka rawa wajen taimakawa sake ginin yankuna da yakin basasar kasar suka lalata a shekarun baya.