Yan kasar syria na adawa da rahoton Mdd | Labarai | DW | 24.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan kasar syria na adawa da rahoton Mdd

Dubbannin mutane a kasar Syria na gudanar da zanga zangar adawa da rahoton da Mdd ta fitar game da rasuwar tsohon faraministan kasar Labanon, wato Rafik Hariri da kuma wasu mutane sama da dozin daya.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa masu zanga zangar na nuna adawar ne a sabili da zargi da rahoton yayiwa wasu fitattun jami´ai na kasar ta Syria.

Bugu da kari rahotannin sun shaidar da cewa masu zanga zangar na nuna wannan boren ne ga rahoton dauke da hotunan shugaba Bashir Al Assad.

Rahoton dai da Mdd ta fitar karkashin jagorancin mai gabatar da kara dan kasar Jamus wato Detlev Mehlis, na dauke da zargi ga wasu fitattun jamia´ai na kasar ta Syria da labanon da cewa da hannun su ne aka tashi bom din daya halaka tsohon faraministan na Labanon wato Rafik Hariri a watan fabarairun shekarar data gabata.