`Yan kasar Holland sun yi watsi da kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai. | Siyasa | DW | 02.06.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

`Yan kasar Holland sun yi watsi da kundin tsarin mulkin Kungiyar Hadin Kan Turai.

Al'umman kasar Holland sun bi sahun na Faransa, wajen yin watsi da kundin tsarin mulkin Kungiyar EU. A zaben raba gardamar da aka gudanar a kasar a ran 1 ga watan Yuni, kashi 61% ne suka jefa kuri'un kin amincewa da kundin.

Firamiyan kasar Holland Balkenende, a lokacin da yake jefa kuri'arsa a zaben raba gardamar.

Firamiyan kasar Holland Balkenende, a lokacin da yake jefa kuri'arsa a zaben raba gardamar.

Tambayar da masharhanta da dama ke yi ne, wai shin wannan hukuncin a’a da `yan kasar Holland suka yanke wa kundin tsarin mulkin kasashen kungiyar Hadin Kan Turai, yana da nasaba kuwa ga rashin amincewarsu ma da manufofin kungiyar ne gaba daya ? Duk dai wanda ya yi nazarin sakamakon binciken ra’ayin jama’a da aka gudanar kafin zaben, zai tabbatar cewa, hawar kujerar na ki da `yan kasar Netherlands din da na Faransa suka yi, ba kawai saboda rashin amincewarsu da kundin tsarin mulkin ba ne. Babu shakka, kundin, wanda shi ne zai kasance kamar wata matashiya ga tsarin tafiyad da halin rayuwar `yan kasashen kungiyar, yana da wuyar ganewa ga masu karatunsa. Sabili da haka ne kuwa, mafi yawan al’umman nahiyar Turan, ba su san ma abin da yake kunshe da shi ba.

A zayyane dai, kundin na tabbatar wa al’umman kasashen kungiyar ne, wadanda yawansu ya kai miliyan dari 4 da 50, `yancinsu da zaman lafiya cikin lumana. Ba a taba dai samun kundin da ke kare hakkin bil’Adama a nahiyar Turai kamar wannan ba a tarihin nahiyar. Duk `yan kasashen kungiyar na da damar kare hakkinsu a kasuwannin kwadago inda za su iya kafa kungiyoyi, su kuma yi yajin aiki, su iya zaban aikin da suke son yi. Kundin na kuma kare su daga korarsu daga wurin aiki ba bisa ka’ida ba.

Duk wadannan ka’idojin dai, babu wanda zai ki amincewa da su, musamman ma dai ba `yan kasar Holland din ba, wadanda suka fi `yan wasu kasashen Turan wayewar kai. Amma ka da kuri’ar na ki da suka yi, kamar dai Faransawan, wato wata alama ce suke son sanayawa don bayyana fargabarsu ga rashin samun aikin yi, da tabarbarewar tattalin arziki da kuma rashin samun daidaito a siyasar harkokin waje. A lal misali, idan dan kasar Litueniya, zai yi farin ciki da samun albashin Euro daya a ko wace awa, a ma’aikatar sarrafa motocin Volvo a kasar Sweden, yayin da `yan kasar da kansu za su rasa guraban ayyukansu a masana’antar, to fa ba za su rungumi tarfarkin nan na kau da shinge a kasuwannin kwadago ba. kungiyoyin kwadago da dama na kasashen Turai ma, sun yi zanga-zangar nuna adawarsu ga wannan manufar a birnin Brussels, abin da ya sa ma ke nan kungiyar ta janye tsarin da ta shirya na kayyade harkokin tsai da albashi a kasashe mambobinta.

Masu sukar lamiri dai na ganin cewa, hawar kujrerar na ki da `yan kasar Holland din suka yi a zaben raba gardamar na jiya, tana da jibinta ne da shigo da kudin nan na Euro, wanda ya janyo tsadar kayayyakin halin rayuwa.

Sakamakon zabukan raba gardama a kasashen Holland da Faransan dai na nuna cewa, jama’ar ba su da cikakkun bayanai kan yadda ababa ke wakana a nahiyar Turan gaba daya. Kazalika kuma, `yan siyasa na duk kasashen kungiyar sun gaza shawo kan masu tantama da manufofinta. A halin yanzu dai, abin da za a fi bukata a kasashen kungiyar ne zaman lafiya, da samar wa al’umma aikin yi, da yaki da habakar kasuwar shunku da kuma fadakad da jama’a game da rashin tushen fargabar da suke yi na barkewar ambaliyar baki a kasashensu.

A sabbin kasashen da suka shigo cikin kungiyar dai, ana iya ganin ci gaban da suka samu tun shigowarsu. Gwamnatocin kuma na fadakar da jama’ansu kan taimakon da suka samu daga kungiyar wajen gina tituna, da makarantu da kuma inganta harkokin noma. Ta hakan ne dai al’umman kasashe kamarsu Sloveniya, da Poland da Hungary ke sane da duk fa’idar da shigar kasashensu cikin kungiyar ke janyo musu. Da an dau wadannan matakan ne a tsoffin kasashen kungiyar, da watakila manoman Faransa alal misali, ba su jefa kuri’ar na ki ba a zaben raba gardamar.

A halin yanzu dai, sakamakon wadannan zabukan ya haifad da wata sabuwar muhawara a kan neman da kasar Turkiyya ke yi na shiga cikin kungiyar. Ra’ayoyin da wasu bangarori ke bayyanarwa, na a dakatad da rattaba hannu kan yarjejeniyar karbar kasashen Bulgeriya da Romeniya cikin kungiyar ma, wata sabuwar damuwa ce ga shugabannin kungiyar a birnin Brussels.

 • Kwanan wata 02.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbX
 • Kwanan wata 02.06.2005
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvbX