1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan kabilar Igbo na bikin cikar Biafra shekaru 50

May 30, 2017

A yau Talata ake cika shekaru 50 da ayyana kudu maso gabashin Najeriya a matsayin kasa mai zaman kanta wanda gwamnan mulkin soja na wancan lokaci Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya yi.

https://p.dw.com/p/2dqZg
Nigeria pro-Donald-Trump-Kundgebung der Indigenous People of Biafra in Port Harcourt
Hoto: Getty Images/AFP

Ko da shi ke ana danganta yakin Biafra da yakin basasa wanda ya  lamushe rayukan mutane miliyan biyu da rabi, amma kuma har yanzu matasan yankin na ci gaba fatan makoma na gari. Amma Kingsley Okah matashi mai shekaru 27 da haihuwa ya karanci kimiyyar siyasa da ke birnin Enugu, babban birnin gwamnatin da aka ayyana Biafra a matsayin kasa tsakanin 1967 zuwa1970.  A yanzu ma dai Kingsley na begen ganin yakin Kudu-maso-gabashi ya balle daga Najeriya, saboda ya na ganin cewar an mayar da Igbo saniyar ware, kuma ya dora wannan alhaki a kan gwamnatin Muhammadu Buhari, musulmi da ya zo daga Arewa.

"A cikin masu rike da manyan mukamai a gwamnatin da ke ci yanzu babu asalin kabilar Igbo ba su dayawa. Saboda haka ne 'yan bokonmu suka dauki mataki daya: Dole ne mu yi yaƙi, domin mu samar wa kanmu 'yancin. Samar da kasar Biyafara ne dai mafita."

Nigeria Biafra | Kingsley Okah
Kingsley Okah, mai fafitikar kafuwar Biafra Hoto: DW/K. Gänsler

Wannan bukata ta aware dai ta mamaye zukatan matasa da dama na yankin kudu maso gabashin Najeriya. Ko da tashoshi tsayuwar bas-bas, wasu hotunan da ke like nasa a tuna da 30 ga watan Mayun 1967, ranar da tsohon gwamnan mulkin soja Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu ya ayyana kasar Biafra, bayan juyin mulki biyu da kuma tsananin rikicin kabilanci. Amma kuma a 'yan shekarun nan samar da kasar Biafra ya zama wani batu da jama’a ke tattaunawa a kan titi.

Ba wani bane ya sake mayar da bara bana tun 2015 ba, illa Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar 'yan asalin Biafara. Gwamnati ta kama shi bisa zargin yin zagon kasa kan hadin kai da kungiyoyin da ke aikata muggan laifuka. Sai dai kuma ya fito daga kurkuku a watan Afirilu, bayan da aka bada belinsa. Sai dai bai hana Kanu a hirarsa da tashar DW, jaddada cewa zai ci gaba da fafutuka domin samar da kasar Biafra ba.

"Rayuwa ba za ta inganta ba tare da kasar Biafra ba . Mun rayu a Najeriya har na tsawon shekaru 56, amma ba mu samu wani ci gaba ba. Muna son bude sabon babi, shigen rayuwa kafin zuwan turawan mulkin mallaka na Birtaniya, inda babu yake-yake,  sannan mun gudanar da addininmu yadda ya kamata."

 Duk irin wadannan kalamai dai, amma a hirarsa da DW game da 'yancin kan Biafra, Kingsley Okah ya bayyana cewar ba a bukatar zubda jini:

"Ba zan dauki makamai don in yi yaki ba. Mun fi bukatar gwagwarmayar ilimi don samar da kasar Biafra. Za a iya wayar da kawuna ta hanyar rubuce-rubuce a jaridu. Wani abin da zai iya taimakawa shi ne, mutane su shirya zanga-zanga, amma ba tare da makamai ba."

Babu dai alkaluma kan yawan mutanen da ke son ganin an kafa kasar Biafra: Sannan gwamnatin Najeriya ta ce shirya zaben raba gardama kan wannan batu bai ma taso ba, saboda Najeriya kasa daya ce al’umma daya.