′Yan jihadi sun sallamo ma′aikatan CICR a Mali | Labarai | DW | 22.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

'Yan jihadi sun sallamo ma'aikatan CICR a Mali

A wannan Jumma'a ne kwamitin agaji na kasa da kasa na CICR, ya sanar da sallamo wasu ma'aikatansa guda uku da aka sace a yankin Arewacin kasar Mali.

Da yake sanar da wannan labari ta shafinsa na Twitter shugaban kwamitin na kasa da kasa na CICR Peter Maurer ya sanar cewa, labari mafi mahimmanci da suka samu shi ne na cewa ma'aikatan na su guda uku da aka sace an sallamo su, kuma su na nan cikin koshin lafiya. A baya dai 'yan kungiyar masu jihadi na Ansar Dine ne suka yi ikirarin sace wadannan ma'aikata tare da neman a sallamo mu su wani mutuminsu da dakarun kasar Faransa suka kama a yankin Arewacin kasar ta Mali.

A hannu daya kuma jami'an tsaro na musamman na kasar ta Mali sun cafke wani dan kasar Mauritaniya mai suna Fawaz Ould Ahmeida, da ake zaton shi ne ya kitsa hare-haren da aka kai a kasar ta Mali, sannan kuma ya na shirya wasu sabin hare-haren a nan gaba.