Yan Jarida na cikin halin tsaka mai wuya a Somalia | Siyasa | DW | 30.01.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yan Jarida na cikin halin tsaka mai wuya a Somalia

Shekarar 2007 ta kasance mafi tsanani ga yan jarida a ƙasar Somalia. Yan jaridar da dama sun rasa rayukan su a hare-haren bama bama bamai.

default

'Yan jarida masu ɗaukar hoto

Ko da a yan ƙwanakin da suka wuce yan jarida takwas ne suka riga mu gidan gaskiya a rikicin na Somalia wanda yaki ci yaki cinyewa. Kusan dai har yanzu babu abin da ya sauya a wannan kasa. Hassan Kafi Hared dan jarida dake aiki da kamfanin ndillancin labarai na kasar Somalia da likitoci biyu daya dan kasar Kenya da kuma dan kasar Faransa tare da Direban su na daga cikin wadanda suka gamu da ajalin su a kwananan yayin da wani bom da aka dana ya tarwatsa motar su a kudancin birnin Kismayo. Shugaban sashen Afirka na kungiyar kare hakkin yan jarida Reporters without Borders Leonard Vincent ya baiyana harin da cewa babban abin takaici ne. Leonard yace za mu cigaba da yin Allah wadai za kuma mu cigaba da ɗaukar bayanan mawuyacin halin da yan jaridan Somalia suke aiki a ciki musamman a Mogadishu. A yau lamarin ya ƙazanta ya kai matsayin yadda mahukunta basa iya yin komai, sai dai ɓaɓatu na fatar baki. Ya zama wajibi shugabannin siyasa dana addini da shugabannin aluma da hukumomi da duk masu riƙe da madafan iko, su yi abin da ya kamata wajen kare yan jarida a Somalia.
To da yake yanzu shugabannin kasashen Afirka zasu hallara a Addis Ababa domin gudanar da babban taron su, ko shin akwai hangen alámura za su inganta ba tare da an dauki matakan siysa da kuma na tsaro don shawo kan matsalolin ba ? Ai ko kusa domin ko wane irin yaƙi sai da matakai na siyasa ake iya kawo ƙarshen sa, domin ko da yaƙin duniya na biyu, ai ba wai an kawo ƙarshen sa bane don an ragargaza Jamus ba, har ma da matakan sasantawa ta fuskar siyasa wanda ya haɗa da yan jarida da suka bada gudunmawa. Saboda haka bamu ga yadda hakan ba zai yiwu ba a Somalia. Ko da yake ba hurumin mu bane mu ce ga wanda gwamnatin riƙon ƙwaryar Somalia za ta yi magana da shi ko kuma waɗanda ya kamata ta yi sulhu da su, amma abin da muke cewa shine matuƙar ana yaƙi, to akwai ƙaídoji na yaƙi kuma waɗannan dokoki kullum ana karya su tsakanin yan ƙungiyar Islama da sojojin Habasha. Amma abin da baá gane ba shine cewa yan jaridar Somalia sune kaɗai ƙungiya ko hukumomi yan ƙalilan da suka haɗa kan su, suka riƙe Somalia a lokacin da kowa ya ɗimauce da game da yaƙi, a kuma lokacin da ƙasar ta rabu a ruɗanin jagorancin madugan yaƙi.
Shekaru goma sha biyar yan jaridar Somalia suna riƙe da haɗin kan ƙasar domin tabbatar da cigaban dimokraɗiyya, amma a yau irin sakayyar da zaá yi musu kenan, sun zama sune mutanen da ake bi ana kashewa. Wannan babban zalunci ne na ƙasar Somalia da kuma Afirka.