1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

’Yan jami’iyyar Socialist ta Faransa, sun zaɓi mace a karo na farko tamkar ’yar takararsu, a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.

Jam’iyyar Socialist ta Faransa ta zaɓi ’yar takara mace, wadda za ta tsaya wa jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a shekarar bara. Jami’ai uku ne suka nemi zamowa ’yan takarar jam’iyyar. Amma a ƙarshe sai mafi yawan mahalarta taron suka zaɓi Ségolène Royal, mai shekaru 53 da haihuwa, tamkar ’yar takarar da za ta yunƙuri gaje gurbin shugaba Chirac. Kusan dai kashi 60 da ɗigo 6 na waɗanda suka ka da ƙuri’un ne suka amince da Madame Royal.

Masharhanta dai sun ce wannan shi ne karo na farko da wata mace, ta taɓa tsayawa takara, inda kuma take da kyakyawar hanyar zamowa shugaban kasar Faransa. Bayan ba da sakamakon zaɓen, Madame Royal ta yi kira ga ’yan ƙasar Faransan da su haɗA kai wajen rungumar sauyin da ake samu a ƙasar da kuma a duniya.

„Yau ina kiran duk Faransawa, maza da mata na wanna ƙasar tamu, da su haɗa kai su zage dantse, wajen bai wa Faransa damar tikarar ƙalubalen da ke gabanta gangane da canje-canjen da ake samu a duniya baki ɗaya, amma ba tare da yin sakaci da jigonmu ba, wato ’yanci, da adalci da ’yan’uwantaka.“