´Yan Islama na kasar Somalia sun ce ba zasu saduda ba | Labarai | DW | 29.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan Islama na kasar Somalia sun ce ba zasu saduda ba

´Yan Islama a Somalia sun ce ba zasu yi saranda ba a fadan da suke yi da gwamnatin wucin gadin kasar dake samun daurin gindin Ethiopia. Sheikh Mohammed Ibrahim Bilal ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP daga birnin Kismayo, cewa janyewar ´yan Islaman daga Mogadishu ba ta nufin kawo karshen wannan rikici. Ya ce nan da kwanaki kalilan komai zai canza. Bilal ya fadi haka ne yayin da dakarun gwamnatin Somalia dake samun kariya daga tankoki da jiragen yakin Ethiopia suka kama birnin Mogadishu. Yanzu haka FM Ali Mohammed Gedi ya ce za´a kafa dokar ta baci ta tsawon watanni 3 a wani mataki na hana shiga cikin rudami bayan da ´yan Islama suka fice daga Mogadishu. Gedi yayi kira ga ´yan Somalia da su hada kai da gwamnati a kokarin ta na maido da bin doka da oda a cikin kasar baki daya. A wani labarin kuma jiragen saman yakin Ethiopia sun yi shawagi a sararin samaniyar birnin Kismayo.