´Yan Islama a Somalia sun gindaya sharadi kafin su tattauna da gwamnati | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

´Yan Islama a Somalia sun gindaya sharadi kafin su tattauna da gwamnati

Shugaban sojojin sa kai na Islama dake iko da Mogadishu babban birnin Somalia ya ce ba zai tattauna batun samar da zaman lafiya da gwamnati ba har sai Habasha ta janye dakarunta daga kasar ta Somalia. Gwamnatin wucin gadin karkashin jagorancin shugaba Abdullahi Yusuf na da mazauninta a garin Baidoa, inda rahotanni suka nunar da cewa sojojin Habasha na tsaron muhimman gine-ginen gwamnati. Gwamnati a birnin Addis Ababa dai na marawa shugaba Yusuf baya, amma ta musanta cewar ta tura dakarunta zuwa Somalia. Da farko dai gwamnati ta amince ta shiga wannan tattaunawa a Sudan, don amsa kiran da MDD ta yi na hana barkewar yaki a wannan kasa dake yankin kahon Afirka.