Yan Iraqi sun kai Blackwater gaban kuliya | Labarai | DW | 12.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Iraqi sun kai Blackwater gaban kuliya

Iyalan wadanda suka rasa rayukan su a Iraqi hannun jami´an tsaron kamfanin nan na Blackwater, sun kai karar kamfanin gaban wata kotu dake birnin Washinton. Ko da yake, iyalan basu fadi cajin da suke wa kamfanin ba, to amma bayanai sun shaidar da cewa kamfanin ya take hakkokin fararen hulan da suka rasa rayukan nasu.Bugu da kari, cibiyar dake radin tabbatar da tsarin doka ta kasa da kasa tace,kamfanin na Blackwater yayi karan tsaye ga dokokin Amurka a lokacin gudanar da aikin tsaron a kasar ta Iraqi, wanda hakan a cewar cibiyar ya kai ga kisan fararen hulan da basu ji basu gani ba. Mutane 17 ne dai suka rasu a lokacin harbe harben da jami´an tsaron kamfanin na Blackwater suka yi a ranar 16 ga watan satumbar wannan shekara.Tuni dai kamfanin tsaron na Blackwater mai zaman kansa ya karyata wannan zargi da ake masa.