Yan Hizboulla na gudanar da zanga zanga a Beirut | Labarai | DW | 01.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yan Hizboulla na gudanar da zanga zanga a Beirut

Dubbannin mutane a Beirut na gudanar da zanga zangar yin Allah wadai da gwamnatin kasar Lebanon, wacce ke samun goyon bayan kasashen yamma.

Zanza zangar wacce yan kungiyyar Hizboulla dake goyawa Syria baya suka shirya, an bayyana cewa ta samu halarcin dubbannin mutanen kasar.

A lokacin zanga zangar, kungiyyar ta Hizboulla ta soki lamirin gwamnatin kasar tare da Allah wadai da ita, da cewar yar koron kasar Amurka ce.

Tuni dai Faraministan kasar, Foaud Siniora yace babu gudu babu jada baya, game da matakan da gwamnatin kasar ke dauka.